in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta aiwatar da shirin inganta sufuri na shekaru 3
2018-06-26 09:35:26 cri

Ma'aikatar sufurin kasar Sin ta ce, kasar za ta aiwatar da wani shirin inganta sha'anin sufuri na shekaru 3.

Wannan shiri zai kara tabbatar da manufar kasar Sin game da gina cikakken tsarin sufuri nan da shekarar 2020, yayin da zuwa lokacin ne kasar ke fatar cimma burinta na gina wata al'umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni.

Nan da shekarar 2020, kasar Sin za ta samar da hanyar jirgin kasa mai saurin tafiya kimanin kilomita dubu 30, wanda za ta hade kashi 80 bisa 100 na biranen kasar mai yawan jama'ar da ta zarta biliyan 1, kamar yadda ma'aikatar sufurin kasar ta sanar.

Kasar Sin tana kuma burin samar da wasu sabbin tashoshin ruwa masu zurfi kimanin 180 wadanda za su iya daukar manyan jiragen ruwan dakon kaya sama da dubu 10.

A cewar wannan shirin, ana kokarin samar da wani tsari ga fasinjoji na yin amfani da tikiti guda wanda za'a iya amfani da shi a zirga zirga mai yawa, ciki har da sufurin jiragen sama, da jirgin kasa mai saurin tafiya da jirgin kasa mai zirga zirga a manyan birane.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China