in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda aka tsai da ra'ayoyin shugaba Xi Jinping kan harkokin waje a matsayin jagora ga ayyukan diplomasiyya ya karfafa gwiwar jami'an diplomasiyyar kasar
2018-06-25 14:33:53 cri






Kwanan baya, an gudanar da taron kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis mai mulki ta kasar Sin kan ayyukan diplomasiyya na kasar, inda babban sakataren kwamitin kuma shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi. Bayan taron, wasu jakadun kasar Sin da suka halarci taron sun bayyana cewa, cikin shekaru sama da biyar da suka wuce, kasar Sin ta cimma manyan nasarori a fannin ayyukan diplomasiyya ne a sanadin jagorancin ra'ayoyin shugaban game da yadda za a gudanar da ayyukan diplomasiyyar kasar bisa tsarin gurguzu a cikin sabon zamanin da muke ciki.

"Jawabin shugaba Xi Jinping ya karfafa mana gwiwa sosai, inda ya yi bayani a kan halin da kasar Sin ke ciki da kuma yadda za a gudanar da ayyukan diplomasiyya bisa tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin cikin sabon zamani, inda kuma baya ga waiwayen ayyukan da aka gudanar a baya, ya kuma yi hasashen makomarsu tare da samar da alkibla ga ayyuka na gaba."

Jawabin Mr. Cui Tiankai jakadan kasar Sin a kasar Amurka ke nan, inda ya yi nuni da cewa, idan aka waiwayi bunkasuwar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka cikin shekaru gomai da suka wuce, duk da matsalolin da aka fuskanta, amma huldar na ci gaba. A game da huldar da ke tsakanin kasashen biyu a halin yanzu, matsayin kasar Sin a bayane yake kamar kullum, ya ce, "babu shakka muna fatan Amurka za ta zama abokiyar hadin gwiwar sauran kasashe a yayin da muke raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, amma ita Amurka tana da 'yancin zabar abin da take so. A ganina, abin da Amurka ke fuskanta shi ne ko za ta gane cewa duniyarmu ta bambanta a cikin karni na 21, kuma a cikin wannan sabon yanayin da ake ciki, ko za ta iya yin watsi da manufar yakin cacar baki tare da rungumar hadin gwiwar samun nasarar juna.?"

In an waiwayi bunkasuwar ayyukan diplomasiyya na kasar Sin cikin shekaru biyar da suka wuce, huldar da ke tsakanin kasar Sin da Rasha ta samu ci gaba mai faranta rai. Shugabannin kasashen biyu sun yi namijin kokarin ta bangaren jagorancin bunkasuwar huldar kasashensu. Yadda kasashen biyu suke girmamawa juna tare da aiwatar da hadin gwiwa cikin daidaici da goyon bayan juna a kan manyan harkokin duniya ya kasance misali ga raya huldar kasa da kasa tare kuma da ba da gudummawar kiyaye kwanciyar hankalin duniya. Jakadan kasar Sin a kasar Rasha, Li Hui ya ce, bunkasuwar huldar da ke tsakanin Sin da Rasha ta samu ne daga ra'ayoyin shugaban kasar Sin kan ayyukan diplomasiyya da kuma jagorancin shugabannin kasashen biyu, ya ce, "muna tuntubar mutane daga sassa daban daban na Rasha a kai a kai, inda muka gane kyakkyawan matsayinsu kan inganta huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. Yayin da aka gudanar da binciken sauraron ra'ayoyin al'ummar Rasha, in aka tambaye su wace kasa ce ta fi kulla zumunta da Rasha, su kan ce kasar Sin ne. Wannan nasara ce da aka samu a sanadin ra'ayoyin shugaban kasar Sin kan ayyukan diplomasiyya da kuma jagorancin shugabannin kasashen biyu."

Jakadan kasar Sin a kasar Zimbabuwe Huang Ping a nasa bangaren ya bayyana cewa, a jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ya yi bayani game da inganta hadin gwiwar kasar Sin da kasashe masu tasowa, inda ya jaddada cewa, kasashe masu tasowa sun kasance kawayen kasar Sin a harkokin duniya, kamata ya yi a kiyaye manufar "cimma muradu da kuma martaba ka'idoji", don hada kan kasashe masu tasowa. Ya ce, "manufar cimma muradu da martaba ka'idoji da kuma manufar kasar Sin kan kasashen Afirka ta sahihance da gaskiya" wani muhimmin bangare ne na ra'ayoyin shugaba Xi Jinping kan ayyukan diplomasiyya, haka kuma alkibla ce da muke bi wajen bunkasa hadin gwiwa da kasashen Afirka. Mu da kasashen Afirka muna da makomar bai daya, kuma abin da za mu yi shi ne mu hada bunkasuwar kasar Sin da taimakawa kasashen Afirka samun ci gabansu, don sassan biyu su taimakawa juna, don samar wa al'ummar sassan biyu moriya.

Har wa yau, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu ya bayyana cewa, yanzu haka ana samun sauye-sauye a harkokin duniya, kuma a daidai wannan muhimmin lokaci ne shugaban kasar Sin ya yi hangen nesa ya gabatar da jerin muhimman manufofi da shawarwari, wadanda suka ba da gudummawar kasar Sin wajen warware matsalolin da duniya ke fuskanta.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China