in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Darajar kamfanonin kafafen watsa labaran Sin a kasuwa za ta kai triliyan 3 nan da 2020
2018-06-25 10:04:31 cri

Wani rahoton da jami'ar Tsinghua ta fitar ya nuna cewa, ana sa ran darajar kamfanonin kafafen watsa labaran kasar Sin za ta kai zai yuan trillion 3 kwatankwacin dala biliyan 460 nan da shekarar 2020.

Rahoton ya nuna cewa, darajar ta karu da kashi 16.6 bisa 100 zuwa yuan trillion 1.9 a shekarar 2017.

Farfesa Cui Baoguo na jami'ar ta Tsinghua ya ce, sakamakon bunkasuwar da aka samu na tsoffin hanyoyin sadarwa da na intanet a halin yanzu, kamfanonin yada labarun sun kasance a matsayin muhimmin bangare na samar da tattalin arzikin kasar Sin ta hanyar ci gaban zamani.

Cui ya kara da cewa, Sinawa suna kashe makudan kudade a bangaren yada labaru da al'adu.

Rahoton ya ce, Sinawa masu bukatar yin sayayya ta intanet, da masu son biyan kudade don tallafawa harkokin ababen bautarsu, suna taimakawa ne ga bunkasuwar kamfanonin sadarwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China