in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban CPPCC ya yi kira da a kara karfafa tsarin jam'iyya a majalisar CPPCC
2018-06-25 09:29:26 cri
Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin Wang Yang, ya yi kira da a kara karfafa tsarin jam'iyya a harkokin majalisar ta CPPCC.

Wang, shugaban taron CPPCC karo na 13 da ragowar jagororin jam'iyyar ne suke yi wannan kiran yayin wani taron karawa juna game da yadda za a gina jam'iyyar da ya gudana ranar Jumma'ar da ta gabata.

Wang, mamban tsayayyen kwamitin hukumar kula da harkokin siyasar kwamitin koli na JKS, ya ce kara karfafa tsarin jam'iyya a harkokin majalisar ta CPPCC, yana daga cikin matakan juyin-juya hali kan bunkasa tsarin gurguzu na musamman mai sigar kasar Sin.

Don haka jami'in na kasar Sin ya yi kira da a aiwatar da shawarwari da tsare-tsaren kwamitin kolin na JKS da ma ka'idojin da ta shimfida game da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar ta Sin.(Ibrahim) 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China