in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mikel zai buga wasan Najeriya da Argentina duk da raunin da yake fama da shi
2018-06-25 09:10:42 cri
Rahotanni daga Rasha na cewa, mai yiwa kyaftin din tawagar Supers Eagles ta Najeriya Mikel Obi zai buga wasan da Najeriyar za ta fafata da kasar Argentina a gobe Talata, duk da raunin tsagewar kashin da ya samu a hannunsu na hagu.

Dan wasan mai shekaru 31 wanda ke buga tamolla a kulob din Tianjin TEDA na kasar Sin, ya ji raunin ne ana dab da tashi d wasan da suka yi nasara da ci 2 da nema a kan kasar Iceland ranar Jumma'a.

Mai horas da 'yan wasan na Najeriya Gernot Rohr ya bayyana a sakon hoton bidiyo wanda hukumar kwallon kafan kasar ta Najeriya ta wallafa a ranar Lahadi cewa, kyaftin din 'yan wasan ya ji rauni, amma zai iya yin wasa.

Idan har Najeriya ta yi nasara ko canjaras a wasan na ranar Talata da Argetina, ko kuma idan Croatia da doke Iceland za ta iya kaiwa zagaye na gaba. Yanzu haka dai tawagar likitocin Super Eagles din na duba raunin da dan wasa ya ji da zummar shiga fafatawar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China