in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mambobin kungiyar OPEC da sauran kasashe masu samar da danyen mai sun yanke shawarar kara fitar da danyen mai
2018-06-24 16:50:34 cri
Jiya Asabar, kungiyar kasashe masu arzikin mai ta OPEC da kasashe masu fitar da danyen mai wadanda ba su cikin kungiyar sun yanke shawara a birnin Vienna cewa, za su kara adadin danyen mai da suke fitarwa tun daga watan Yuli mai zuwa.

Cikin taron da aka yi a wannan rana, mambobin kungiyar ta OPEC da sauran kasashe masu fitar da danyen mai, ciki har da Rasha sun tsaida kudurin fitar da karin danyen mai domin biyan bukatun kasuwannin duniya.

Haka kuma, cikin sanarwar da suka fitar, an ce, a watan Mayu na bana, adadin raguwar danyen mai da kungiyar OPEC da sauran kasashe masu samar da danyen mai suka yi ya riga ya kai kashi 147 bisa dari na burin da aka tsara wajen rage adadin fitar da danyen mai, ya kamata a mayar da adadin a matsayin kashi 100 bisa dari.

Haka kuma, a ranar 22 ga wata, mambobin kungiyar OPEC sun cimma matsaya guda a yayin taron ministocin man fetur, inda suka yanke shawara cewa, za su kara adadin danyen man da suke samarwa a kowace rana tun daga wata mai zuwa. Amma ba a fitar da cikakken daftarin aiwatar da wannan aikin ba, wato adadin danyen man da kowace mamba ta kungiyar za ta kara samarwa. Lamarin da ya sa, ake ganin cewa, mambobin kungiyar ba su cimma ra'ayi daya ba kan wannan batu.

A karshen shekarar 2016, kungiyar OPEC da sauran kasashe 11 wadanda suke samar da danyen mai, ciki har da kasar Rasha sun kulla yarjejeniyar rage adadin danyen man da suke fitarwa, wato an rage ganga miliyan 1.8 a kowace rana, domin warware matsalar adadin danyen mai da ake fitarwa a kullum wanda ake ganin ya zarta bukatun kasuwannin duniya.

Bisa labarin da aka samu, an ce, a halin yanzu, wasu mambobin kungiyar suna gamuwa da matsalar samar da danyen mai, lamarin da ya sa danyen mai da kungiyar OPEC take fitarwa bai kai adadin da aka tsara ba. Kana, bisa karuwar bukatun kasa da kasa kan danyen mai, kiran da gamayyar kasa da kasa suka yi na kara adadin danyen man da za a fitar yana ta karuwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China