in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi: Nacewa ga jagorancin tunanin harkokin waje bisa tsarin gurguzu mai halayyar kasar Sin don bude sabon shafin harkokin wajen kasar
2018-06-23 20:25:42 cri

Ana gudanar da taron aikin kula da harkokin waje na kwamitin koli na jam'iyyar JKS a nan birnin Beijing tsakanin ranekun 22 zuwa 23 ga wata, inda babban sakataren kwamitin kolin JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, dole a nace ga jagorancin tunanin harkokin waje iri na tsarin gurguzu mai halayyar kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki yanzu, ta yadda za a kara fahimtar yanayin da ake ciki a kasar Sin da kuma fadin duniya, kana za a kara mai da hankali kan aikin farfado da al'ummar kasar Sin tare da sa kaimi kan ci gaban bil Adama, a sa'i daya kuma za yi kokarin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga bil Adama da kiyaye ikon mulkin kasa da tsaro da moriyar kasar, a karshe dai, ya ce za a bude wani sabon shafi ga aikin harkokin waje mai halayyar musamman ta kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China