Petteri Taalas ya ce a cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata, Sin ta zama ja gaba a duniya, a fannin samar da hidimar yanayi da fasahohi, kuma fasahohin da Sin ta samar a wannan fanni, sun zama abin koyi ga sauran kasashe membobin hukumar kula da yanayi ta duniya.
A nasa bangaren, mukaddashin jakadan Sin dake zaunannen ofishin kasar a MDD da sauran hukumomin duniya dake birnin Geneva Fu Cong, ya bayyana cewa, yana maraba da karin kasashen duniya da su shiga hadin gwiwar yanayi bisa tsarin "ziri daya da hanya daya" don samun moriyar juna tare. (Zainab)