in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka sojoji 16 yayin da dakarun dake da sansani a gabashin Libiya suka yi yunkurin karbe iko da wasu tashoshin mai
2018-06-22 21:02:19 cri

Wata majiya ta jami'an lafiya a kasar Libiya, ta ce sojoji 16 sun rasa rayukan su, yayin wani fada da ya barke a garin Ajdabiya mai arzikin mai dake gabashin kasar, lokacin da sojojin dake da sansani a gabashin kasar suka yi dauki ba dadi da dakarun dake hamayya da su, a yunkurin su na kwato wasu tashoshin ajiyar mai.

An ce baya ga dakarun sojin da suka rasu a jiya Alhamis, fadan ya kuma sabbaba jikkatar wasu 20. Bayan dauki ba dadin, dakarun soji dake yankin gabashin kasar, sun yi nasarar kwace wasu tashoshin ajiyar mai dake yankin guda biyu daga abokan hamayyar su masu dauke da makamai.

Majiyar jami'an lafiyar yankin ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sashen lura da masu bukatar gaggawa, ya amshi gawawwaki 16, tare da wadanda suka jikkata 20. A daya hannun kuma an hallaka masu dauke da makamai 50, wadanda ake sa ran kungiyar ba da tallafin jin kai ta "Red Crescent" za ta aike da jami'an ta domin kwaso gawawwakin su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China