in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kaddamar da bikin fina finan kasa da kasa na Sin da Afirka karo na 2 a Afirka ta kudu
2018-06-22 20:13:53 cri

Yau Juma'a ne aka kaddamar da taron watsa labarai, game da bikin fina finan kasa da kasa na Sin da Afirka karo na biyu a birnin Shanghai na kasar Sin. Babban gidan rediyo da telibijin na kasar Sin, da hadin gwiwar kwalejin fina finai ta birnin Beijing ne za su shirya bikin.

Yayin bikin, mataimakin babban editan gidan rediyon kasar Sin CRI Ren Qian ya bayyana cewa, a watan Oktoban bara, aka gudanar da bikin karo na farko a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu. Kuma baya ga kara sha'awar 'yan kallo game da fina finai na kasashen Afirka da fina finan kasar Sin, bikin ya kuma kara karfafa fahimtar juna dake tsakanin masu aikin fina finan sassan biyu wato na Sin da Afirka. Kaza lika bikin ya kara habaka tasirin fina finan Sin da Afirka a fadin duniya. A don haka za ci gaba da gudanar da bikin karo na biyu a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu tsakanin ranekun 7 zuwa 10 ga watan Oktoban bana.

Darekta mai kula da aikin sayar da fina finai na bikin Jehad Kasu, shi ma ya bayyana cewa, bikin zai kara karfafa cudanyar al'adu dake tsakanin sassan biyu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China