in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen V4 da Austria sun tattauna kan batun 'yan gudun hijira
2018-06-22 14:49:22 cri
Firaministocin kungiyar Visegrad (V4) sun gana da takwaransu na kasar Austri, inda suka kira wani taro a jiya, birnin Budapesti. Firaministan kasar Hungary Orbán Viktor ya ce, kasashen mahalarta taron sun cimma matsaya daya kan karfin da kasashen Turai suke da shi don tsaron iyakokinsu da kiyaye mazaunansu.

A yayin wani taron manema labarai da aka yi bayan taron, Orbán Viktor ya ce, kamata ya yi kasashen Turai su tabbatar da dangantakar dake tsakaninsu a matsayin hadin kai, maimakon gaba da juna. A ganinsa, ya kamata kasashen su mai da hankali kan wasu batutuwan da za su iya kai wa ga matsaya daya game da matsalar 'yan gudun hijira, alal misali tsaron iyakar kasa da kafa sansanin 'yan gudun hijira a wajen rukunin EU da sauransu. A wani bangare kuma, kada a tilastawa sauran kasashe kan wasu batutuwan da ba a cimma matsaya daya kan su ba, kamar yawan adadin 'yan gudun hijira da za a karba. An ce V4 za su bayyana ra'ayoyinsu kan batun 'yan gudun hijira a taron koli na EU karo na 28.

Firaministan Slovakia Peter Pellegrini shi ma ya nuna cewa, ya kamata a mai da hankali kan tsaron iyakokin EU a wajen rukuni, ta yadda za a tabbatar da tsaron nahiyar Turai.

Ban da wannan kuma, firaministan kasar Austria Sebastian Kurz ya ce, Austria za ta rike da shugabancin karba-karba na EU daga ran 1 ga watan Yuli mai zuwa, abin da ya fi muhimmanci a ganinta shi ne manufar tsaro da lafiya, musamman ma batun yaki da kwararar 'yan cin ran. Ya ce, idan babu tsaro a iyakokin wajen rukunin Turai, to ba za su iya bude iyakokinsu a cikin rukunin EU ba.

An ba da labarin cewa, ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar 1991 ne, Hungary, Poland da Czechoslovakia suka hada kansu don kafa wata kungiyar shiyya-shiyya. Saboda an gudanar da wannan taro a Visegrad, sai ake kiransu da kungiyar Visegrad, kuma bayan rabuwar Czech da Slovakia, kungiyar ta kunshi da kasashe hudu. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China