in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shigar da ra'ayin al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya cikin takardar nasarar taron sararin samaniyar MDD
2018-06-22 14:34:47 cri

An kira taro bisa babban matsayi na cika shekaru 50 da shirya taro karon farko na bincike da amfani da sararin samaniya cikin lumana na MDD, tsakanin ranekun 20 zuwa 21 ga wata a Vienna. A cikin takardar sakamakon taron, an karbi shawarar da kasar Sin ta gabatar, inda ta yi kira da karfafa hadin kan kasa da kasa a fannin amfani da sararin samaniya ta hanyar lumana, da nufin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga duk bil'adama.

Yayin wannan taron bisa babban matsayi na cika shekaru 50 da shirya taron bincike da amfani da sararin samaniya cikin lumana na MDD, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Vienna, mista Shi Zhongjun ya ba da jawabi cewa, burin da ake fatan cimmawa na ganin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma a fannin sararin samaniya ba dacewa da buri da manufar yarjejeniyar sararin samaniya kadai ya yi ba, har ma da bincike da amfani da sararin samaniya don samar da moriya, da biyan bukatun da ake da su a yanzu haka wajen kiyaye muhallin sararin samaniya, da inganta ayyukan sararin samaniya da neman dauwamammen ci gaban tattalin arziki da al'umma. Baya ga haka, ya tabbatar da burin da za a cimma a fannonin karfafa gudanarwa da hadin kan kasa da kasa ta fuskar sararin samaniya, da tinkarar kalubale daban daban da ake fuskanta wajen amfani da sararin samaniya cikin lumana. Mista Shi ya ce,

"Bincike da amfani da sararin samaniya sha'anin bai daya ne na duk bil'adama. Ya kamata bil'adama su hada kai don bincike da amfani da sararin samaniya ta hanyar lumana, da nufin neman moriyar bai daya. An kuma shigar da wadannan muhimman manufofin cikin yarjejeniyar sararin samaniya, kana sun kasance ginshiki na gudanar da harkokin sararin samaniya. Baya ga haka, kamata ya yi a nemo makomar sararin samaniya nan gaba, da karfafa kwarewar bil'adama ta bincike sararin samaniya, domin sanya kasashe da mutane mafi yawa su ci gajiyarsa."

Ban da wannan kuma, mista Shi ya bayyana hakikanin manufofi da matakai da kasar Sin ke dauka wajen karfafa hadin kan kasa da kasa, da kyautata ayyukan gudanar da harkokin sararin samaniya bisa ra'ayin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga duk bil'adama. Wannan ra'ayin da Sin ta gabatar ya samu karbuwa daga wajen wakilan kasashe da dama da suka halarci taron. Paolo Nepoli, 'dan saman jannatin kasar Italiya, wanda ya taba zama a tashar sararin samaniyar kasa da kasa ya yi tunani kan abubuwan da yake ji a sararin samaniya.

"Idan ka zura ido kan sararin samaniya, za ka yi mamaki sosai sakamakon fadinsa, aikin binciken sararin samaniya na shafar kowa da kowa, shi ne sha'anin bai daya na duk bil'adama. Ko da yake kasa na da muhimmanci, amma moriyar bai daya ta bil'adama ta fi muhimmanci. A nan gaba, ya kamata dukkan kasashe su tattara albarkatu da fasahohi da hazakarsu, don habaka amfani da sararin samaniya ta hanyar hadin kai. Lallai, akwai abubuwan da yawa da har yanzu ba mu sani ba."

Bayan tattaunawar da aka yi tsakanin bangaori daban daban, takardar sakamakon taron, ta karbi shawarar da kasar Sin ta gabatar, inda aka yi kira da karfafa hadin kan kasa da kasa a fannin amfani da sararin samaniya ta hanyar lumana, da nufin kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga duk bil'adama, ta hakan za a samar da alheri da moriya ga duk bil'adama. An dai zartas da takardar bayan shirye-shirye da shawarwari da aka yi shafe tsawon shekaru 3 ana yi, kuma kasashe mambobin MDD suka zartas da ita baki daya, za kuma a gabatar da ita ga babban taron MDD karo na 73, don zartaswa. Daraktar ofishin kula da harkokin sararin samaniyar MDD Simonetta Di Pippo ta bayyana a gun taron cewa,

"Bincike da amfani da sararin samaniya ta hanyar lumana, ginshiki ne wajen ciyar da zaman al'umma da tattalin arziki gaba, ya kamata kasashe daban daban su karfafa hadin kai a fannin, don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, da nufin cimma burin neman dauwamammen ci gaba kafin shekarar 2030, kana da inganta gine-ginen muhimman na'urorin sararin samaniya."

An shirya taron na kwanaki biyu ne domin tunawa da cika shekaru 50 da kiran taron bincike da amfani da sararin samaniya cikin lumana karo na farko da MDD ta yi a shekarar 1968, kana da nazarin nasarorin da aka cimma da kalubalen da ake fuskanta a fannin ayyukan sararin samaniya, tare kuma da tsara shiri kan ayyukan gudanar da harkoki a fannin a nan gaba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China