in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da mahalartan taron kolin kwamitin CEO na duniya
2018-06-21 21:21:48 cri

Yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da jagororin manyan kamfanonin kasashen duniya, wadanda ke halartar taron kolin kwamitin CEO na kasashen duniya a nan kasar Sin, ya kuma tattauna da su.

Xi ya yi nuni da cewa, tun daga bara, tattalin arzikin duniya ta samu farfadowa sannu a hankali, amma bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, kuma kasar Sin tana son yin kokari tare da sauran kasashen duniya domin cimma burin samar da kyakkyawar makoma ga bil Adama.

Xi ya kara da cewa, tun daga lokacin da aka gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, kafin shekaru biyar da suka gabata, al'ummun kasa da kasa sun samu moriya daga shawarar. Ya kuma jaddada cewa, jarin waje yana taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China