in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Borno: Mutane 15 sun ji raunuka sakamakon harin kunar bakin waje a wata barikin sojoji
2018-06-21 19:18:31 cri

Rahotanni daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa, mutane 15 sun jikkata, yayin da wasu 'yan kunar bakin wake 2 suke tada ababen fashewa a wata barikin sojoji dake jihar.

Harin dai na ranar Laraba ya haifar da hargitsi a barikin, kuma duka 'yan kunar bakin waken biyu sun rasa rayukan su yayin harin. An dai ce maharan mata ne, kuma sun yi nufin tada ababen fashewar ne a wata mashaya dake cikin barikin.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edet Okon, ya ce sojoji sun harbe 'yar kunar bakin wake ta farko, yayin da take kokarin sayen tikitin shiga babbar kasuwar dake cikin barikin. Ita kuwa 'yar kunar bakin wake ta biyu, ta tada abun fashewar ne a cikin wani babur mai kafafu 3.

Mr. Okon ya ce, kawo yanzu ba a tabbatar da ko dukkanin wadanda suka jikkatan sojoji ne ba ko a'a. Jami'in ya ce tuni aka mika wadanda suka jikkata zuwa asibitin gwamnati domin samun kulawar kwararru.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China