in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron ministoci karo na biyu kan matakan tinkarar sauyin yanayi
2018-06-21 14:39:04 cri






A jiya Laraba, aka bude taron ministoci karo na biyu kan matakan tinkarar sauyin yanayi a birnin Brussels, hedkwatar kasar Belgium, kuma kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai da kuma Canada ne suka hada kai don shirya taron. Wakiliyarmu Lubabatu na tare da karin haske.

Taron na yini biyu ya samu halartar ministoci da manyan jami'ai daga kasashe 35, inda suka yi musayar ra'ayoyi tare da daidaita matsayin juna a game da sakamakon da ake sa ran cimmawa a gun taron yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 24 da za a gudanar a birnin Katowice na kasar Poland a watan Disamba mai zuwa da ma sauran batutuwan da suka shafi tabbatar da yarjejeniyar Paris. A wajen bikin bude taron, wakili mai kula da sauyin yanayi da makamashi na kungiyar tarayyar Turai Miguel ARIAS CAÑETE ya gabatar da jawabin cewa, tarayyar Turai da Canada da Sin ne suka sake shirya wannan taron biyowa bayan taron ministoci da aka shirya a karo na farko a bara a birnin Montreal na kasar Canada, don yin kira ga kasa da kasa su himmantu wajen tinkarar sauyin yanayin duniya, ya ce, "Taron ya bayyana aniyarmu ta aiwatar da yarjejeniyar Paris da neman gano bakin zaren warware matsaloli ta hadin kan sassa daban daban. Muna sa ran taron zai cimma sakamakon da ya dace da manufar Paris, kuma tarayyar Turai da Sin da Canada na da niyyar ci gaba da hadin gwiwa da masu yarjejeniyar Paris a kokarin cimma wannan buri."

A nasa jawabin, wakilin musamman na kasar Sin kan batun sauyin yanayi Mr. Xie Zhenhua ya bayyana cewa, tsarin taron ministoci kan matakan tinkarar sauyin yanayi yana da inganci, wanda ke iya taka rawa mai yakini ta bangaren tabbatar da yarjejeniyar MDD. Sai dai ya jaddada cewa, duk da cewa a kokarin da sassa daban daban suka yi, ana aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata, amma akwai rashin tabbas da ake fuskanta ta fannin manufofin siyasa da suka shafi kulawa da sauyin yanayin duniya. A sa'i daya kuma, ana kara fuskantar kalubale ta fannin tinkarar sauyin yanayi. Ya yi nuni da cewa, "Domin tinkarar kalubalen, ya kamata kasa da kasa su hada kansu, kuma su yi iyakar kokarinsu, sa'an nan a jibanci kokarin tinkarar sauyin yanayi da kiyaye muhalli da ayyukan bunkasa tattalin arziki da kawar da talauci da kyautata rayuwar jama'a da samar da guraben ayyukan yi da kiwon lafiya da kuma kiyaye zaman lafiya, a sauya hanyar da ake bi na bunkasa tattalin arziki ya zama mai kiyaye muhalli."

Mr. Xie Zhenhua ya kuma jaddada cewa, kiyaye muhalli sabon yayi ne da ake bi, wanda kuma ya yi daidai da manufar kasar Sin ta tabbatar da ingancin bunkasuwar tattalin arziki da kara karfin kiyaye muhalli. A baya bayan nan, gwamnatin kasar Sin ta yiwa hukumominta kwaskwarima, inda aka kafa ma'aikatar kiyaye muhalli, matakin kuma da zai taimaka ga hada karfin sassa daban daban wajen tabbatar da yarjejeniyar Paris, don tinkarar sauyin yanayi tare kuma da kiyaye muhalli. Ya ce, "A gun taron kiyaye muhallin kasar Sin da aka kira a watan Mayun wannan shekara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kamata ya yi a aiwatar da manufofin tinkarar sauyin yanayi, sa'an nan a sa kaimi wajen kafa tsarin kulawa da yanayin duniya wanda ya kasance mai cike da adalci da kuma samun moriyar juna, don daukar nauyin dake wuyan kasar Sin. kasar Sin za ta tabbatar da alkawuran da shugabanta ya dauka, kuma za ta ci gaba da hada kai da sassa daban daban na duniya, don sa kaimin cimma nasarar taron Katowice da ke tafe, a kokarin kiyaye muhallin duniyarmu."

Ministar kiyaye muhalli da tinkarar sauyin yanayi ta kasar Canada, Madam Catherine McKenna ma ta gabatar da jawabi a gun bikin bude taron, inda ta ce, tinkarar kalubalen da duniyarmu ke fuskanta na bukatar hada kan kasashen duniya, ya kamata mu yi kokari tare. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China