in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna rashin jin dadi ga kudurin Amurka na ficewa daga hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD
2018-06-20 19:46:50 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi yau Laraba cewa, har kullum kasar Sin tana goyon bayan tsarin hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, haka kuma tana kokarin sa kaimi, da kuma kiyaye hakkin dan Adam a fadin duniya.

Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta, ga kudurin da kasar Amurka ta yanke game da ficewa daga hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD, kuma Sin za ta ci gaba da taka rawar da ta dace a fannin raya aikin kare hakkin dan Adam tare da sauran kasashen duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China