A cikin wata wasikar da wadannan kungiyoyin suka gabatar, sun bayyana cewa, a matsayinsu na wakilin dake wakiltar moriyar sassan masu samar da kayayyaki da masu sayar da kayayyaki da kamfanonin kimiyya da fasaha da manoma da kuma kamfanonin amfanin gona da dai sauransu, suna nuna damuwa sosai kan hanyar da gwamnatin ke dauka na warware bambamcin ra'ayi ta fuskar ciniki wato kara kakabawa sauran kasashen haraji da kayyade kason cinikin shigo da kayayyaki.
Kuma sun yi gargadi cewa, barazana tsakanin Amurka da abokan cinikinta da ya kara yin tsami zai haddasa yanayi maras tabbaci sosai, karin harajin da gwamnatin ta kakabawa kayayyakin da take shigowa daga sauran kasashe da martanin da kasashen suka mayar zai kawo illa ga bunkasuwar tattalin arzikin Amurka, har ma zai kara yawan kudin da kamfanoni da iyalan Amurka za su kashe nan gaba. (Amina Xu)