in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ba da umurni kafa rundunar tsaron sararin samaniya
2018-06-19 16:16:09 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ba da wani umurni a jiya, inda ya nemi hukumar tsaron kasar da ta kafa rundunarta ta shida wato sabon nau'i na rundunar tsaron sararin samaniya.

Yanzu haka kasar Amurka na da nau'o'in rundunar soja guda biyar wato rundunar sojin kasa, da rundunar sojin sama, da ta sojin ruwa, da rundunar Marine Corps da kuma rundunar tsaron iyakar teku.

A cewar Trump, kamar yadda kasa ne, sama da teku suke, sararin samaniya ma na iya zama fagen yaki. Shawararsa ta sami amincewa daga wasu 'yan majalisar dokokin kasar, sai dai wasu sun nuna shakku ga lamarin.

Trump ya kara da cewa, Amurka na bukatar rike jagorancin harkokin sararin samaniya domin kiyaye tsaronta. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China