in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masaniyar OECD: tsayawar kasar Sin kan bude kofarta ga duk duniya na da muhimmanci sosai ga kokarin bunkasa duniyar baki daya
2018-06-19 11:43:58 cri


ana shekara ce da ake cika shekaru 40 da kaddamar da manufar kasar Sin ta yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga ketare. Madam Margit Molnar, direktar ofishin nazarin manufofin tattalin arzikin kasar Sin ta kungiyar hadin gwiwa da bunkasa tattalin arziki, wato OECD wadda ta taba shan bincike a kasar Sin, ta zama wadda take gano yadda kasar Sin take samun sauye-sauye cikin 'yan shekarun baya. A kwanakin baya, a lokacin da take ganawa da wakilinmu dake kasar Faransa, ta bayyana masa ra'ayinta kan yadda manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare da kasar Sin ta kaddamar, ke yin tasiri ga kokarin bunkasa duniya baki daya.

A lokacin da take ambato tasirin manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga duk duniya, madam Margit tana ganin cewa, da farko dai, ana iya gano babbar gudummawar da manufar ta bada ga tattalin arzikin duniya kai tsaye. Madam Margit ta ce, "A ganina, gudummawa mafi muhimmanci ita ce gudummawa ga karuwar tattalin arzikin duk duniya. Ko da yake yanzu saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya ragu kadan, amma har yanzu yawan gudummawar da take ba tattalin arzikin duk duniya ya wuce kashi 1 bisa 3, kuma ba za a iya canja wannan yanayi da ake ciki, cikin matsakaicin lokaci mai zuwa ba. Sabo da haka, a ganina, gagarumar gudummawar da manufar kasar Sin ta yin gyare-gyare da bude kofa ta ga duk duniya ta bayar ita ce, karuwar tattalin arzikin duk duniya."

A lokacin da ake bunkasa tattalin arziki, ana canza tunani da hanyar neman bunkasuwa da kasar Sin take bi sakamakon wannan manufar yin gyare-gyare da bude kofa. Sannan sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin yin gyare-gyaren tsarin tattalin arzikinta yana kuma da muhimmanci ga sauran kasashen duniya, ciki har da kasashe masu tasowa. A ganin Margit, abin da yafi muhimmanci ga bunkasar tattalin arzikin kasar Sin shi ne, tana kokarin bunkasa tattalin arziki bisa bukatun da ake da su a kasuwa. "Sannan, a ganina, tana kokarin bunkasa tattalin arzikinta bisa bukatun da ake da su a kasuwa maimakon bisa shirin gwamnati, wannan wani babban canji ne kan tsarin tattalin arziki, ko da yake har yanzu ba a kammala wannan canji ba, amma a lokacin da take canza shi, an yi kokarin yin amfani da bukatun mutune, ingancin bunkasa tattalin arziki zai kara samun kyautatuwa sannu a hankali."

Bayan da ta yi dimbin shekaru tana yin gyare-gyare da bude kofa, kasar Sin ta riga ta kubutar da kanta daga halin fama da talauci. Sakamakon haka, manyan matsalolin da take fuskanta yanzu suna kuma canzawa. Alal misali, gibin dake tsakanin masu arziki da marasa arziki ya tsananta. Game da matsalar, madam Margit tana ganin cewa, ya kamata gwamnati ta kara karfi a fannonin karbar haraji da nuna goyon baya. "Ya kamata masu arziki su biya karin haraji, sannan za a iya yin amfani da wannan haraji wajen tallafawa masu fama da talauci. Bugu da kari, ya kamata a kara mai da hankali kan zaben masu fama da talauci wadanda a hakika dai suke bukatar tallafi daga gwamnati. Sabo da haka, a ganina, ya kamata gwamnati ta kara tsara manufofin ba da tallafi da na karbar haraji."

Yanzu kan kasar Sin na hade da sauran kasashen duniya sosai sakamakon kaddamar da manufar yin gyare-gyare da bude kofarta ga duk duniya. A 'yan shekarun nan, shawarar bunkasa "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar na taka muhimmiyar rawa ga kokarin bunkasa duk duniya baki daya. Game da shawarar, madam Margit ta bayyana cewa, irin wadannan shawarwari na shafar fannoni daban daban, ba fannonin tattalin arziki da cinikayya kadai ba. Ta ba da wani misalin cewa, za a iya kara yin hadin gwiwa a fannin kare ikon mallakar fasaha bisa shawarar bunkasa "ziri daya da hanya daya".

A yayin kaddamar da taron tattaunawar Asiya na Boao da aka yi a watan Afrilun bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin za ta kara fadada bude kofarta da ta riga ta bude ga duk duniya maimakon rufe ta. Madam Margit ta yi imanin cewa, duk duniya za su samu moriya sakamakon matakin kara bude kofa da kasar Sin take dauka, har ma da samun karin damar neman ci gaba. "A idona, yanzu duk duniya na maraba da manufar bude kofa da kasar Sin take dauka. Yanzu kasar Sin ta kasance kamar kungiyar tattalin arziki mafi girma ta biyu a duk duniya. Idan ta kara bude wannan babbar kasuwa ga duniya, duk duniya za su ci gajiya." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China