Rundunar tsaron hadin gwiwa ta Iraqi, ta ce dukkan jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda na Hashd Shaabi na tsare da iyakokin kasar, ciki har da wadanda ke kan iyakar Iraqi da Syria, kuma babu wani luguden wuta ta sama ko wani hari da ya auka musu.
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa an kai harin ne kan hedkwatar tsaro dake yankin al-Hiri dake yankin kudancin al-Bukamal na gabashin Syria, wanda ke da lambuna da gidaje dake da nisan kilomita 1.5 daga iyakar Iraqi da Syria.
Da farko a ranar, rundunar Hasd Shaab ta fitar da wata sanarwa, inda ta ce 22 daga cikin mambobinta sun mutu, wasu 12 kuma sun jikkata, sanadiyyar wani hari da take zargin rundunar kawance da Amurka ke jagoranta ta kai sansaninta dake cikin Syria, wanda ke kusa da iyakar Iraqi. (Fa'iza Mustapha)