in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya goyi bayan shirin tsakaita bude wuta na gwamnatin Afghanistan da mayakan Taliban
2018-06-19 10:58:32 cri
A jiya Litinin kwamitin tsaron MDD ya nuna goyon baya ga sanarwar da gwamnatin Afghanistan ta fitar a karshen mako, inda ta nemi tsawaita wa'adin yarjejeniyar tsakaita bude wuta na wucin gadi tsakanin gwamnatin da mayakan kungiyar Taliban bayan kammala hutun Idin karamar sallah.

Cikin wata sanarwa da kwamitin ya rabawa manema labarai ya ce, mambobin kwamitin sulhun MDDr sun nuna rashin jin dadinsu kasancewa Taliban ba su sanar da aniyarsu na tsawaita yarjejeniyar tsakaita bude wutar na wucin gadi ba, inda ta bukace su da su amince da bukatar da gwamnatin ta gabatar na aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar tsakaita bude wutar.

Mambobin kwamitin tsaron MDDr sun bukaci Taliban da ta amince da tayin da gwamnatin Afghanistan din ta yi musu, tun a watan Fabrairun wannan shekara ne gwamnatin ta bukaci Taliban su amince su shiga tattaunawar sulhu don wanzar da zaman lafiya ba tare da gindaya wasu sharruda ba.

Gwamnatin Afghanistan ta sanar a ranar 7 ga watan Yuni cewa, ta amince da yarjejeniyar tsakaita bude wuta na wucin gadi wadda ta fara aiki daga ranar 12 ga watan Yuni har zuwa karshen kammala bukukuwan Idin karamar sallah, daga bisani kuma ta ayyana karin kwanaki 10 na tsakaita bude wutar daga bangarenta. Kungiyar Taliban dai ta amince ne da yarjejeniyar tsakaita bude wutar na wucin gadi na tsawon kwanaki 3 a lokacin hutun bukuwan karamar sallah amma ta ki amincewa da tsawaita wa'adin. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China