in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ba ta amince da raba 'ya'yan 'yan cin rani da iyayensu ba
2018-06-19 10:03:53 cri
Babban sakataren MDD António Guterres, ya ce majalisar ba ta amince da tilasta raba iyaye 'yan cin rani da yaransu ba.

Sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya yi a jiya, ta ruwaito Antonio Guteres na cewa, ya kamata a mutunta hakkin 'yan gudun hijira da 'yan cin rani, tare da daidaita matsalolinsu bisa dokar kasa da kasa. Ya kara da cewa, kada a wahalar da zuciyar yara saboda tilasta raba su da iyayensu, kuma kamata ya yi a kiyaye hadewar iyalansu.

A wani taron manema labarai da ya gudana a jiyan, Dujarric ya ce, Guterres ya bayyana matsayinsa ne bai wai yana nuna yatsa ga wata kasa ba, yana mai cewa Sakatare Janar din ya damu matuka da rikicin daya faru a iyakar Amurka da Mexico.

Rahotanni na cewa, cikin makonni 6 da suka gabata, an tilasta raba yara kimanin 2000 da iyayensu dake tsallakawa ba bisa ka'ida ba daga Mexico zuwa Amurka. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China