in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa na murnar bikin wasan kwale kwale
2018-06-18 15:43:46 cri

Yau Litinin 18 ga wata,wadda ta yi daidai da ranar 5 ga watan Mayu bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, rana ce ta bikin Duanwu wato bikin wasan kwale kwale na Sinawa, a don haka Sinawa a fadin kasar ke murnar bikin ta hanyoyi daban daban, misali shirya gasar kwale kwale, da samar da abinci irin na wainar Zongzi, da wanka cikin ruwan maganin gargajiya na kasar Sin, yayin da wasu kuma ke tuka mota zuwa wurare daban daban domin bude ido.

Bikin Duanwu yana da dadadden tarihi na tsawo shekaru dubu biyu, an ce a zananin da, wani mai rubutun wakoki da ake kira da sunan Qu Yuan ne ya jefa kansa cikin ruwan kogi a wannan rana, domin nuna kishinsa ga kasa. Daga baya ne kuma aka kebe wannan rana a matsayin ta bikin kasa domin tunawa da Qu Yuan. Bikin Duanwu da bikin bazara da bikin share kaburbura da bikin tsakiyar kaka sun kasance manyan bukukuwa hudu na kasar Sin.

Ya zuwa shekarar 2009, bikin Duanwu na kasar Sin ya samu amincewar hukumar kula da harkokin ba da ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD UNESCO, inda ya zama daya daga cikin muhimman al'adun gargajiyar kasashen duniya. Bikin da ya zama al'ada irinta ta farko a kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China