in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta yi gargadin fuskantar gurbacewar muhalli bayan barkewar rikici a yanki mai arzikin mai
2018-06-17 16:31:34 cri

Hukumar dake kula da albarkatun mai ta kasar Libya (NOC) ta yi gargadin fuskantar barazanar gurbacewar muhalli bayan wani tashin hankalin da ya barke a yanki mai arzikin mai na kasar.

A wata sanarwa da NOC ta fitar ta ce, rikicin ya haifar da lalacewar wata tankar mai a tashar ruwa ta Ras Lanuf, sai dai ba ta yi cikakken bayani game da irin mummunar illar da lamarin zai iya haifarwa ga muhallin ba.

Hukumar ta bukaci a hanzarta janye dakarun 'yan bindiga dake karkashin jagorancin Ibrahim Jathran ba tare da gindaya wasu sharruda ba don kaucewa gurbacewar muhallin da kuma lalata wasu muhimman kayayyakin more rayuwa.

Jathran, wani tsohon jami'in kula da kayayyakin albarkatun mai ne wanda ake nemansa ruwa a jallo.

NOC ta sake yin gargadin cewa, ci gaba da lalata kayayyakin albarkatun man zai iya haifar da mummunar illa a bangaren man kasar ta Libya da ma tattalin arzikin kasar baki daya.

NOC ta bukaci dukkan bangarori da su guji yin amfani da kayayyakin albarkatun man kasar a harkokin da suka shafi rikicin siyasa kuma su kauracewa shigar da bangaren man cikin duk wani tashin hankali. Kana duk wani al'amarin da zai iya jefa rayuwar al'ummar kasar Libyan cikin garari abin yin Allah wadai ne.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China