in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na da niyyar cimma nasarar yakin cinikayya da Amurka
2018-06-16 16:53:25 cri

Ba tare da la'akari da ra'ayin bai daya da ta cimma da Kasar Sin ba, Gwamnatin Amurka a jiya Juma'a, ta fitar da takardar jerin kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 50, da za ta kara karbar harajin kaso 25 cikin 100 kansu.

Bisa kiyaye dokokin da batun ya shafa ne ita ma kasar Sin ta sanar da kara harajin kaso 25 cikin 100, kan kayayyaki 659 da darajarsu ta kai dala biliyan 50, da ke shiga kasar daga Amurka.

Matakin martani da Sin ta dauka ya nuna niyyarta na kiyaye moriyarta da ta jama'arta, tare da kare dunkulewar tattalin arzikin duniya da tsarin cinikayya na bangarori da dama.

A hakika, babu wanda zai cimma nasara sakamakon yakin cinikayya. Amma har kullum, kasar Amurka kan yi amai ta lashe, inda ta kan tayar da yakin cinikayya, wanda ba alkawarin da ta dauka kan jama'ar kasashen Sin da Amurka kadai ta karya ba, har ma da kara harzuka kasashen da suka shigar da wadanda ke son shigar da kararta gaban kotu dangane da batun cinikayya. Kungiyar 'yan kasuwar Amurka da Kungiyar 'yan kiri ta kasar da ta manoman waken soya da sauran kungiyoyi kasuwanci, sun fitar da sanarwa daya bayan daya, inda suka yi zargin cewa, matakin da gwamnatin Trump ta dauka, na kara karbar haraji kan kayayyakin kasar Sin, yunkuri ne na karbar harajin daga masu sayen kayayyaki 'yan Amurka. Har ma farashin waken soya na Amurka, ya ragu zuwa mafi kankanta adadi cikin tsawon watanni 9 da rabi da suka gabata, al'amarin da ke nuna cewa, kasuwar duniya ta damu ainun da yakin cinikayya tsakanin Sin da Amurka.

A matsayin ta na kasa mai son zaman lafiya, da ba da shawarar hadin kai, kasar Sin ba ta son shiga yakin cinikayya, sai dai kuma, ba ta tsoron yakin. Matakin da Amurka ta dauka ya lahanta yanayin cinikayyar kasar Sin da tsarin cinikayyar bangarori da dama na duniya, don haka, kasar Sin ta shiga yakin ba tare da la'akari da asarar da za ta yi ba, da nufin kiyaye moriyar jama'arta da tsarin cinikayyar duniya yadda ya kamata.

Baya ga haka, kasar Sin ta lura cewa, Amurka ta sanar da cewa, idan Sin ta dauki matakan mayar da martani, to za ta kara karfafa yawan harajin, inda ita ma Sin din ta ce za ta dauki matakan martani da matsayi makamancin na Amurka. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China