in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya gana da mataimakiyar firaiministan Sin game da karfafa hulda
2018-06-15 12:13:30 cri
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace kasarsa a shirye take ta karfafa dangantakar raya al'adu da hulda tsakanin mutum da mutum tsakanin Rasha da Sin, ciki har da batun hadin gwiwa a fannin wasanni. Putin ya tabbatar da hakan a lokacin ganawa da mataimakiyar firaiministan kasar Sin Sun Chunlan a jiya Alhamis.

Putin ya bukaci Sun ta isar masa da sakon fatan alheri ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana ya yabawa Sun sakamakon halartar bikin bude gasar cin kofin duniya na hukumar FIFA na 2018 a matsayinta na wakiliyar musamman ta shugaba Xi.

Ziyarar ta Sun ta kara tabbatar da irin yadda kasar Sin take bada muhimmanci da nuna goyon baya game da harkokin wasanni wanda kasar ta Rasha ke karbar bakuncinsa da kuma yadda take fatar ganin cigaban harkokin wasannin kwallon kafa a duniya, inji Putin.

Sun tace shugaba Xi da Putin sun gana a kwanakin baya a Beijing, kuma sun yi musayar ra'ayoyi game da yadda kasashen Sin da Rashar zasu kara zurfafa huldar dake tsakaninsu.

Kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Rasha wajen aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma matsaya kansu da kuma kara karfafa dangantaka a fannin raya al'adu da hulda tsakanin al'ummomin kasashen biyu, inji Sun.

Sun tace tana da tabbacin kasar Rasha zata tafiyar da harkokin karbar bakuncin gasar cin kofin duniyar ta FIFA cikin nasara, kuma zata nunawa duniya irin cigaban data samu ta fuskar tattalin arziki da cigaban zamantakewar al'umma.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China