in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara gasar cin kofin duniya a karo na 21
2018-06-15 11:26:50 cri

A daren jiya 14 ga wata, aka fara gasar cin kofin duniya a karo na 21 a filin wasa na Luzhniki da ke birnin Moscow, hedkwatar kasar Rasha.

Bayan nuna wasannin fasaha, shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino sun gabatar da jawabi. Putin ya bayyana cewa, babban burinsu shi ne, isar da karfi da sakon hadin kai ga zuriyoyinmu, don sa kaimi ga bunkasuwar sha'anin motsa jiki da kiyaye zaman lafiya da kara fahimtar juna tsakanin Bil Adam. Ya ce yana sa ran za a samu nasarori masu armashi a gasar.

Wannan ne karo na farko da Rasha ta karbi bakuncin gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya, kungiyoyin wasan kwallon kafa 32 ne za su fafata a birane 11 na kasar Rashar, inda za a gudanar da gasar ta karshe a ranar 15 ga watan Yuli.

A cikin gasa ta farko, Rasha ta yi wasa cikin hali mai kyau wadda ta doke kunigyar Saudiyya da ci 5-0. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China