Xi Jinping, wanda shi ne shugaban kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin sojan kasar, ya yi wannan jawabi ne yayin da yake rangadi a lardin Shandong na gabashin kasar, daga ranekun 12 zuwa 14 ga wata.
Shugaba Xi ya kuma yi kira da a yi kokarin daukaka darajar masana'antu da kirkire-kirkiren dake inganta ci gaba da inganta kayakin more rayuwa da mayar da Shandong muhimmin lardi da ake zirga-zirgar jiragen ruwa da inganta bude kofa da sauye-sauye, da kuma samun nasara wajen cimma ci gaba mai inganci.
A matsayinsa na babban lardin a fannin aikin gona, shugaba Xi ya ce hakkin Shandong ne, tabbatar da wadatar abinci a kasar, yana mai kira da a kara kokarin samar da kayakin abinci da inganta aikin gona da kara kudin shigar manoma da yaki da talauci da aiwatar da tsarin zamanantar da aikin gona da yankunan karkara da kuma mayar da Shandogon lardin misali na aiwatar da wannan tsari. (Fa'iza Msutapha)