Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, da ministoci, da wakilan kasashen Labarabawa, da kuma babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa ta LA, na cikin wadanda ake fatan za su halarci taron.
Geng Shuang ya kara da cewa, yayin taron, za a gudanar da tattaunawa mai zurfi, game da zurfafa kawance na gargajiya dake tsakanin sassan biyu, da fadada shawarar nan ta ziri daya da hanya daya. Sai kuma batun bunkasa sabon salon kawance na kasa da kasa, da samar da al'umma mai cin gajiyar makoma ta bai daya.
Har ila yau, za a yi amfani da taron wajen dada karfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa karkashin dandalin na CASCF, da ma sauran batutuwa da suka shafi kasa da kasa, da na shiyya shiyya da ke jawo hankulan sassan biyu.