Kafin shawarwarin, Wang ya bayyanawa manema labaru cewa, an cimma nasarar shirya shawarwari tsakanin shugaban kasar Amurka Donald Trump, da takwaransa na kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un a kwanan baya a kasar Singapore.
Wannan ne karo na farko da shugabannin kasashen biyu suka yi shawarwari, don haka yana da ma'ana sosai. Shawarwarin dai sun sanya an mai da warware batun Zirin Koriya kan hanyar da ta dace ta yin shawarwari, wanda hakan ya dace da moriyar bai daya ta bangarori daban daban da batun ya shafa, ciki har da Amurka da Koriya ta arewa.
A hannu guda kuma, kasar Sin ta nuna yabo sosai ga kokarin da bangaren Amurka ya yi, ciki har da Mr. Pompeo. (Bilkisu)