in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaya ake share fagen gasar cin kofin duniya na Rasha?
2018-06-14 13:40:51 cri

Za a gudanar da gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya a kasar Rasha daga ranar 14 ga watan Yuni zuwa ranar 15 ga watan Yulin bana. Manema labaru na kasa da kasa na da babban nauyin sanar da duniya abubuwa dake faruwa a wannan kasaitaciyar gasa. Tambayar ita ce, mene ne abubuwan da ya kamata a mai da hankali a kai a yayin gasar?

Manema labaru fiye da dubu 3 daga sassa daban daban na duniya za su shafe wata guda suna bayar da rahotanni kan gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya karo na 21.

A matsayinta na kasar da ta fi lashe kofin gasar a tarihin gasar, kasar Brazil ta kan jawo hankali a yayin gasar a ko wane karo. Fernando, dan kasar Brazil, ya sha aiko da rahotanni kan gasar cin kofin duniya, inda ya bayyana mana cewa, ana gudanar da ayyukan shirya gasar cin kofin duniya ta Rasha yadda ya kamata. Ababen wasanni da kuma filayen horaswa dukkansu suna da kyau, wadanda suke taimakawa 'yan wasa nuna iyawarsu yadda ya kamata a yayin wasanni, lamarin da zai taimakawa kasarsa ta Brazil zama zakara a kasar ta Rasha. Fernando ya ce,"Ina tsammani, Brazil tana daya daga cikin wadanda ake ganin za su lashe gasar. Kowa ya san cewa, mu kungiyar Brazil muna da karfi sosai. Na yi imani da cewa, tabbas 'yan wasan Brazil za su sake cin kofin duniya a Rasha."

Kungiyar kasar Argentina wadda ke da shahararren dan wasa Leonardo Messi har kullum tana jawo hankalin kasa da kasa. A wannan karo, gomman kafofin yada labaru na Argentina sun je kasar Rasha domin ba da labarai game da gasar, wadanda yawansu ya dara na dukkan kasashen Latin Amurka. Dangane da abun da ya fi burge shi a kan gasar cin kofin duniya ta wannan karo, Petro, dan jaridar Argentina ya bayyana mana cewa,"Na shafe sa'o'i kusan 40 zuwa kasar Rasha a jirgin sama. A ganina, ana gudanar da ayyukan da suka shafi gasar cin kofin duniya yadda ya kamata. Kuma ana gudanar da ayyuka da yawa. Ban da haka kuma, akwai tsaro. An samar da tsaro a kewayen filayen wasa, da tituna, da tashoshin jiragen a karkashin kasa da sauran wuraren taruwar jama'a."

Sakamakon murza gashin baki a tsakanin kasar Rasha da kasashen yammacin duniya a 'yan shekarun baya da suka wuce, ya sa wasu kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya suka shafa wa Rasha kashin kaji. A sakamakon haka kuma, Rashawa suna sa ran ganin jama'ar kasashen Turai da Amurka sun canja ra'ayoyinsu kan kasarsu ta hanyar gudanar da gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya a wannan karo, da kuma kyautata huldar da ke tsakanin kasarsu da kasashen yammacin duniya. Dan jaridar kasar Birtaniya Brad ya yi bayani da cewa, "A kasarmu, labarun da wasu kafofin yada labaru suke bayarwa sun tsoratad da mu dangane da kasar ta Rasha. Amma duk da haka ya zuwa yanzu abubuwan da aka ambata a wadannan labaru ba su abku a kanmu ba tukuna. Dukkanmu muna alla-alla ganin an fara gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya mai kayatarwa."

To, mene ne ra'ayoyin 'yan jaridar kasar Rasha, mai masaukin gasar cin kofin duniya na wannan karo? Dan jaridar kasar Rasha Aleksei yana ganin cewa, kasarsa ta Rasha ta ci gajiya a fannoni da dama sakamakon gudanar da gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya karo na 21. An gina wasu sabbin filayen wasa da dakunan wasa. Bayan haka kuma, an kyautata ababen more rayuwar al'umma kwarai da gaske, kamar su hanyoyi da sufuri. Amma duk da haka ya kaskantar da kansa ya nuna cewa, "Watakila Akwai abubuwan da muka kasa wajen share fagen gasar cin kofin duniya, muna bukatar karin lokaci don tabbatar da su. Alal misali, akwai tazara tsakanin ko wane filin wasa. Sa'an nan kuma ba mu da kwarewa wajen tattara masu sha'awar wasan kwallon kafa cikin gajeren lokaci da kuma tsaro."

Za a gudanar da gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin duniya karo na 21 a filayen wasa guda 12 a birane 11 da ke kasar Rasha daga ranar 14 ga watan Yuni zuwa ranar 15 ga watan Yulin bana. Kasashen duniya suna alla-alla kan gasar, suna sa ran ganin gasanni masu kayatarwa, da jin dadin kallon kasar Rasha mai kyau, da jin dadin gasar cin kofin duniya, da kuma jin farin ciki da wasan kwallon kafa zai kawo musu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China