in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta danganta shawarar ziri daya da hanya daya da ajandar cigaba ta MDDr nan da 2030
2018-06-14 09:43:08 cri

Liu Zhenmin, mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin tattalin arziki da walwalar al'umma ya bayyana cewa, shawarar nan ta ziri daya da hanya daya ta gwamnatin Sin da ajandar MDD ta samar da dawwamamman cigaba nan da shekarar 2030 suna da manufofin da burika iri guda.

"Ko da yake shawarar ziri daya da hanya daya da ajandar MDD ta samar da dawwamamman cigaba nan da shekarar 2030 suna da banbanci da juna ta fuskar yanayinsu da tsarinsu, sai dai suna yin kamanceceniya da juna ta fuskoki da dama, suna da manufofi da buri iri guda, kuma an kafa su ne da kyawawan manufofi," in ji mista Liu. "Dukkanninsu suna yin aiki ne karkashin tsarin dokokin MDD. Dukkaninsu suna da manufar bunkasa tsarin hadin gwiwar moriya tare, da samar da cigaba tare, da makoma mai kyau, da samar da zaman lafiya, da yin hadin gwiwa tare, da bude kofa, da yin aiki tare da juna, da girmama juna da kuma amincewa juna."(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China