in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan majalisun dokokin Afirka ta kudu sun yi kira da a hanzarta binciken dalilin mutuwar ma'aikatan hakar ma'adinai
2018-06-14 09:37:15 cri

Shugabar kwamitin kula da harkokin filaye da albarkatun kasa a majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu Olifile Sefako, ta bukaci ministan albarkatun kasar Gwede Mantashe, da ya hanzarta gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwar wasu ma'aikatan hakar ma'adinai hudu a mahakar Sibanye-Stillwater kusa da birnin Johannesburg.

Mutuwar masu hakar ma'adinan na ranar Litinin da dare ya kawo adadin masu hakar ma'adinai 19 da suka halaka a mahakar yayin da suke bakin aiki daga watan Janairun wannan shekara zuwa yau, baya ga wasu ma'aikata guda 9 da aka ba da rahoton mutuwarsu a watanni biyu da suka gabata.

'Yan majalisar dokokin dai sun zargi hukumomin dake kula da aikin hakar ma'adinai da rashin tsara wasu muhimman dokoki da matakan kare rayukan ma'aikata. Suna mai cewa, yadda masu aikin hakar ma'adinai da dama ke rasa rayukansu a lokacin aiki, alama ce dake nuna cewa, akwai bukatar daukar wasu matakan da suka dace don magance wannan matsala. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China