in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin ya yi kira da a kara goyon-bayan harkokin nakasassu a kasashe masu tasowa
2018-06-13 20:34:50 cri
A yayin taro karo na 11 na kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kare hakkin nakasassu wanda aka yi jiya Talata, jakadan kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya, Ma Zhaoxu, ya ce ya kamata bangarori masu ruwa da tsaki su inganta hadin-gwiwarsu, a kokarin ciyar da harkokin da suka shafi nakasassu gaba a duk fadin duniya.

Ma ya ce, kashi 20 bisa dari na mutane mafiya talauci nakasassu ne, adadin da ya kunshi kashi 80 bisa dari dake zaune a kasashe masu tasowa. Don haka ya zama dole a rubanya kokarin tallafawa kasashe maso tasowa, musamman ma kasashe mafiya fama da kangin talauci.

Game da matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka, Ma ya ce, gwamnatin kasarsa na maida hankali sosai kan moriyar jama'arta, da jagorantar ayyukan tallafawa nakasassu dake kunshe da bangarori daban-daban. Haka kuma gwamnatin Sin na karfafa gwiwar bangarori da yawa, domin su shiga cikin ayyukan da suka jibanci nakasassu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China