A cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, Mr. Pompeo zai gudanar da ziyarar ne bisa gayyatar da babban dan majalissar zartaswar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi masa.
Geng Shuang ya kara da cewa, sassan biyu za kuma su yi musayar ra'ayi, game da dangantakar dake tsakanin kasashen su, tare da muhimman batutuwan da suka shafi kasa da kasa, dana shiyya shiyya, wadanda suke jan hankalin sassan biyu.