in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Koriya ta arewa da Amurka sun gana da juna a Singapore
2018-06-13 13:51:59 cri

A ranar jiya Talata da safe, shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong un da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump suka gana a Otel din Capella da ke kasar Singapore, ganawa ta farko a tsakanin shugabanni masu ci na kasashen biyu kafin daga bisani su kaddamar da shawarwari, shugabannin biyu sun kuma gana da 'yan jarida tare, inda Shugaba Trump ya yi imanin cewa, shawarwarin za su yi nasara matuka.

"Ina sa ran kyakkyawan fatan kan yadda za mu tattauna da juna. Ina ganin cewa, tattaunawarmu za ta yi nasara matuka. Lallai wannan abin farin ciki ne a gare ni, za mu raya dangantakar kud-da-kud a tsakaninmu."

Shi ma a nasa bangare, Shugaba Kim ya bayyana cewa, bangarorin biyu sun gana da juna ne bayan haye wahalhalu iri daban daban.

"Lallai mun yi sa'ar gaske da muka iso nan. Tarihi na baya kamar sarkokin da aka daura a kafafunmu. Tsohon bambamcin ra'ayi ma ya kawo cikas ga ci gabanmu. Amma a karshe dai mun haye duk wadannan wahalhalu, mun sadu da juna."

Daga baya shugabannin biyu sun yi shawarwari su biyu da kuma masu tafinta kawai, inda suka shafe mintoci 45. Sa'an nan kuma tawagogin kasashen biyu sun yi shawarwari a tsakaninsu na tsawon mintoci kimanin 100. Da misalin karfe 1 da minti 40 na yammacin ranar kuwa, shugabannin biyu sun sake ganawa da 'yan jarida, inda suka sanar da cewa, za su rattaba hannu kan wata yarjejeniya.

Shugaba Trump na kasar Amurka ya furta cewa,

"Muna shirin sanya hannu kan wata yarjejeniya mai matukar muhimmanci, wadda ta shafi fannoni daban daban. Mun yi hira sosai, kuma mun raya dangantakarmu yadda ya kamata. Sanya hannu kan wannan yarjejeniya wani abin farin ciki ne ga dukkanmu."

A nasa bangaren kuma, Shugaban Kim ya yi tsokacin cewa,

"Za mu yi watsi da abubuwan da suka faru a baya domin rattaba hannu kan wannan yarjejeniya mai ma'ana a tarihi. Duniya baki daya za ta ga babban canji. Ina godiya ga Shugaba Trump saboda amincewa da wannan ganawa a tsakaninmu."

Rahotanni na cewa, yarjejeniyar ta kunshi alkawarin da Amurka da Koriya ta arewa suka yi na kafa sabuwar dangantaka a tsakanin kasashen biyu bisa burin jama'arsu na neman zaman lafiya da samun wadata. Ban da wannan, Amurka da Koriya ta arewa za su hada kansu don kafa wani tsarin zaman lafiya mai dorewa a zirin Koriya. Kasar Koriya ta arewa kuma ta nanata Sanarwar Panmunjomon da aka fitar a ranar 27 ga watan Afrilu na shekarar 2018, inda ta yi alkawarin cewa, za ta yi kokarin cimma burin kawar da makaman nukiliya a zirin koriya. Bugu da kari, Amurka da Koriya ta arewa sun yi alkawarin cewa, za su gano gawawwakin fursunonin yaki da wadanda suka bace a lokacin yakin Koriya da aka gwabza daga shekarar 1950 zuwa 1953, da gaggauta dawo da wadanda tuni aka gano.

Haka zakila, a yayin taron manema labarai da Shugaba Trump ya shirya, ya nuna godiya ga kokarin da bangarori daban daban ciki har da shugaban kasar Sin Xi Jinping suka yi domin ganin an samu zaman lafiya a zirin Koriya. Ya kuma bayyana cewa, zai dakatar da atisayen soja tare da kasar Koriya ta kudu. Game da batun, Jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore ta wallafa wani sharhi dake cewa, wannan ya shaida cewa, bangarori daban-daban sun amince da shawarar da kasar Sin ta gabatar, wato Koriya ta arewa ta dakatar da ayyukan da suka shafi nukiliya da makamai masu linzami, Amurka da Koriya ta kudu kuma su dakatar da babban atisayen sojan da suke yi.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China