in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hasashen yawan matsakaicin shekarun haifuwa na Sinawa a shekarar 2017 ya kai 76.7
2018-06-13 13:35:10 cri

Kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin ya ba da wata sanarwa mai jigo "Kidayar bunkasuwar sha'anin kiwon lafiya na Sin na shekarar 2017" a daren ran 12 ga wata.

Wannan sanawa din ta nuna cewa, hasashen yawan matsakaicin shekarun haifuwa na Sinawa a shekarar 2017 ya karu daga 76.5 na shekarar 2016 zuwa 76.7, yawan mutuwar jarirai ya ragu daga kashi 7.5 cikin 1000 zuwa kashi 6.8 cikin 1000, yayin da yawan mutuwar mata masu juna biyu ya ragu daga kashi 19.9 cikin dubu 100 zuwa kashi 19.6 cikin dubu 100, matakin da ya bayyana cewa, alkalumar lafiyar Sinawa ta kai fiye da na kasashen dake da kudin shiga mafi yawa. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China