in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Sin ta taka muhimmiyar rawa mai alfanu kan halin da zirin Koriya ke ciki
2018-06-13 11:10:11 cri

MDD ta bayyana a jiya 12 ga wata cewa, Sin ta taka muhimmiyar rawa mai alfanu kan halin da zirin Koriya ke ciki yanzu.

Stephane Dujarric kakakin sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana hakan ne a gun wani taron manema labarai da aka saba yi a kowace rana.

Antonio Guterres ya mai da ganawa da aka yi a jiya tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Koriya ta arewa Kim Jung-un a matsayin wani muhimmin al'amari a tarihi.

Shugaba Donald Trump da takwaransa Kim Jung Un sun sa hannu kan wata yarjejeniya, inda Koriya ta arewa ta yi alkawarin ba da gudunmawa wajen tabbatar da ganin babu kasancewar makaman nukiliya gaba daya a zirin Koriya. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China