in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNAIDS: Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cutar AIDS
2018-06-13 09:27:07 cri

Babban daraktan hukumar dake yaki da cuta mai karya garkuwa jiki ta MDD UNAIDS, Michel Sidibe, ya ce kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato AIDS.

Jami'in ya bayyana hakan ne a helkwatar MDD bayan da ya gabatar da rahoton irin ci gaban da aka samu a shirin hukumar na kokarin kawar da cutar ta AIDS daga doron kasa.

Babban jami'in ya ce, a kokarin da ake na kwarya kwaryar shirin kawar da cutar nan na shekarar 2020, wanda aka amince da matakin a yayin babban taron MDD a shekarar 2016, ya ce duniya tana samun ci gaba a kokarin da ake na kawo karshen cutar ta AIDS nan da shekarar 2030.

Sidibe ya ce, kasar Sin tana amfani da ilmi a matsayin jigo, da kuma tabbatar da tsabta, wanda ya hada da tsabtar muhalli, da harkokin wasanni dama sauran bangarori wadanda tuni ta riga ta inganta su.

Jami'in MDDr ya ce, dangantakar Sin da Afrika hulda ce mai ban mamaki. Ministocin lafiya na kasashen Afrika suna yin taro domin tattaunawa game da sabbin matakai da za'a bi domin aiwatar da shirin yaki da cutar yadda ya kamata.

Ya ce, kasar Sin ta shiga kasar Saliyo domin taimakawa al'ummun kasashen Afrika wajen kawar da cutar Ebola, ya kara da cewa, Sin ta kasance kasa ce da ta samu nasara wajen samun kwararrun likitoci, wadanda suke taka muhimmiyar rawa wajen horas da jami'an lafiya na kananan yakunan kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China