in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta fitar da manhajan da darajarsu ta kai dala biliyan 37.5 zuwa kasashen waje a 2017
2018-06-13 08:58:34 cri

Wani rahoto da ma'aikatar cinikayyar kasar Sin ta fitar game da harkokin cinikayya ta yanar gizo ya nuna cewa, a shekarar 2017 da ta gabata kasar ta fitar da manhajan da darajarsu ta kai dala biliyan 37.5 zuwa kasashen waje, karuwar kaso 9.7 cikin 100 a kan shekarar da ta gabace ta.

A cewar rahoton, kimanin rabin wadannan na'urori wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 18.9, an fitar da su zuwa kasar Amurka, da kungiyar tarayyar Turai da kuma kasar Japan.

Rahoton ya kara da cewa, tun daga shekarar 2012 zuwa wannan lokaci, yadda kasar ta Sin ke fitar da manhajojin zuwa ketare yana karuwa, har ya kai matsayin koli.

Haka kuma rahoton ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta da karfin kirkire-kirkire na bunkasa kayan gyaran manhajoji, inda ta gargadi kamfanonin samar da manhaja na cikin gida game da karuwar farashi da hadarin dake tattare da masana'antar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China