Ma'aikatar harkokin wajen Sin ta fitar da sanarwa game da ganawar shugabannin Koriya ta Arewa da Amurka
Yau Talata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wata sanarwa, dangane da ganawar da aka yi tsakanin shugabannin kaashen Koriya ta Arewa da na Amurka a kasar Singapore, inda ta ce, ganawar ta yi armashi, har ma ta haifar da sakamako mai kyau, al'amarin da ya kasance babban ci gaban da aka samu ta fannin kokarin kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya, da warware matsalar zirin ta hanyar siyasa.
Kaza lika sanarwar ta bayyana cewa kasar Sin ta jinjinawa shawarar da shugabannin kasashen biyu suka yanke, tare da maraba, da goyon-baya ga sakamakon da aka samu a yayin shawarwarin na su. Har ila yau kuma, ta yabawa matukar kokarin da bangarori daban-daban suka yi game da shirya shawarwarin cikin nasara. (Murtala Zhang)