in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwararta ta Ghana
2018-06-12 19:31:51 cri
Memba a majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi shawarwari da takwarar sa ta kasar Ghana, madam Shirly Ayorkor Botchway jiya Litinin a birnin Beijing.

Wang Yi ya ce, yana farin cikin ganin cewa shugaban Ghana Nana Akufo-Addo zai zo kasar Sin, don halartar taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a watan Satumban bana. Ya ce Sin na yin amfani da dandalin FOCAC tare da Ghana, da kara aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya', da ci gaba da fadada hadin-gwiwarsu, a wani kokari na samar da alfanu ga kasashen biyu, gami da jama'arsu baki daya.

A nata bangaren ma, madam Botchway ta ce, gwamnatin Ghana na maida hankali sosai kan raya dangantakarta da kasar Sin, kuma tana alla-allar wajen koyon yadda kasar Sin ta yi gyare-gyare a gida da neman bunkasuwar ta, da kuma kara aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya', domin ciyar da hadin-gwiwar kasashen biyu gaba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China