Shugaba Kim da Mr. Trump sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa bayan taron su na yau Talata, a zaman da ya wakana a otal din Capella dake tsibirin Sentosa na kasar Singapore.
Cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, shugaba Trump ya ce zai tabbatar da samar da cikakken tsaro ga Koriya ta arewa, yayin da shi kuma shugaba Kim ya nanata aniyarsa, game da kammala dukkanin manufofi da suka shafi raba zirin koriya da makaman nukiliya.