in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mekel: Kamata ya yi Turai ta kara hada kai da kasar Sin
2018-06-12 10:14:08 cri

Shubabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel ta bayyana a ranar Lahadi da dare cewa, ba ta ji dadin abin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi a gun taron koli na G7 ba, a ganinta, Turai ba za ta dogaro da dangantakar dake tsakaninta da kasashen dake gabar tekun Atlantika ba, ya kamata kasashen Turai su dogaro da kansu su kara hada kai a tsakaninsu da kuma kara tutunbar sauran kasashe ciki har da kasar Sin.

Bayan kammala taron koli na G7 da aka yi a jihar Quebec dake kasar Canada, Madam Merkel ta dawo Jamus a daren wannan rana tare inda ta zanta da wani gidan talibijin, tana mai cewa, tana bakin ciki sosai game da shawarar da Trump ya yanke kwatsam ta kin sanya hannu kan hadaddiyar sanarwar G7.

Merkel ta kara da cewa, ba ta son ta yi watsi da ka'idojin G7, amma kamata ya yi Jamus ta yi shawarwari da Rasha, sannan ta kara hada kai da kasashen Japan, Canada, Indiya da kuma Sin. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China