in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da mutane miliyan 5 na fama da munanan cututtuka a Mozambique
2018-06-12 09:24:13 cri

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Mozambique ta bayyana damuwa cewa, sama da mutane miliyan biyar ne a kasar suke fama da cututtuka masu tsanani a halin yanzu.

Ministar kiwon lafiyar kasar Nazira Abdul wadda ta bayyana hakan yayin taron manema labarai, ta ce matsalar canjin yanayi da yanayin zaman jama'a, na daga cikin dalilan da suka haddasa yawan mutanen dake fama da wannan matsala.

Cibiyar harkokin kiwon lafiya ta kasar wadda ta sanar da wadannan alkaluma cikin wani rahoto da ta fitar, ta ce lamarin abin tayar da hankali ne.

Ministar ta ce, kamata ya yi a bullo da managartan matakai da tsare-tsaren hana yaduwar cututtuka masu tsanani da ba yada su da ke tayar da hankalin al'umma.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China