in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD za ta hada gwiwa da nahiyar Afrika don rage tsadar aikewa da kudi nahiyar
2018-06-12 09:18:11 cri
Hukumar aikewa da sakonni ta MDD, ta ce za ta hada hannu da Gwamnatoci a nahiyar Afrika domin rage tsadar aikewa da kudi nahiyar.

Darakta Janar na hukumar Bishar Hussein, ya shaidawa Xinhua jiya a birnin Nairobin Kenya cewa, aikin da ake a yankin na biyan kudin hidimar aikewa da sakonni ta kafafin sadarwa a Afrika, zai ba bangaren aikewa da sakonni na kasashen damar taka muhimmiyar rawa, wajen saukaka aikewa da kudi ga wadanda suka yi kaura zuwa kasashen waje.

Bishar Hussein ya bayyana yayin taro kan sadarwa karo na 25, na yankin gabashin Afrika cewa, za su hada hannu da hukumar kula da kaura ta MDD, domin cin gajiyar dimbin hanyoyin dake akwai a bangaren aikewa da sakonni na gwamnatoci, da nufin rage tsadar aikewa da kudade nahiyar Afrika zuwa kaso 5, ta yadda za a saukaka harkokin da suka shafi kudi. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China