in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen gabashin Afirka sun bayyana sha'awarsu ta shiga kasuwannin kudu maso gabashin Asiya
2018-06-12 09:10:12 cri

Kasashen yankin gabashin Afirka karkashin laimar kungiyar raya yankin gabashin nahiyar (IGAD) sun nuna sha'awarsu ta yin amfabi da yankin Hong Kong na kasar Sin wajen shiga kasuwannin sayar da nama da dabbobi na yankin kudu maso gabashin Asiya.

Wata sanarwa da kungiyar ta IGAD ta fitar a jiya Litinin ta bayyana cewa, a baya kasashe mambobin kungiyar na fitar da dabbobi da nama ne zuwa kasashen Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka (MENA), amma yanzu kasuwar sayar da nama da dabbobi dake yankin Hong Kong zai taimaka wajen magance wasu daga kalubalen da kasashe ke fuskanta yayin fitar da wadannan hajoji zuwa yankin na MENA.

A cewar IGAD, duk da kusanci da albarkatun dabbobi da Allah ya horewa yankin gabashin Afirka, yankin na biyan bukatun kaso 50 cikin 100 na kasuwannin yankin Gabas ta Tsakiya ne, sai kuma kaso 10 cikin 100 na kasuwannin dake yankin arewacin Afirka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China