A cewar AVIC, jiragen biyu sun kammala gwajin da aka yi masu cikin nasara, a wata makarantar horas da matuka jiragen sama dake Afirka ta kudu.
Don haka, nan ba da dadewa za a fara amfani da samfurin jiragen a makarantun horas da matuka jiragen sama, da ma sauran harkoki na sufurin fasinjoji a nahiyar.
Wannan ne dai karon farko da wani samfurin jirgin sama kirar kasar Sin ya shiga kasuwannin Afirka.