in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron kolin kungiyar SCO a birnin Qingdao
2018-06-11 13:55:31 cri

A jiya Lahadi da yamma agogon Qingdao na kasar Sin ne, aka kammala taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) karo na 18 da ya gudana a birnin Qingdao dake gabashin kasar Sin.

A yayin taron kungiyar SCO na wannan karo, shugaban kasar Sin kana shugaban karba-karba na kungiyar na wannan karo, Mista Xi Jinping, ya gabatar da wani jawabi mai taken "Yada Ruhun Shanghai don kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya", inda ya marabci firaministan kasar India Narendra Modi, da shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain, wadanda suka halarci taron SCO a karon farko a matsayinsu na shugabannin kasashe mambobin kungiyar. Shugaba Xi ya ce, taron na bana shi ne taron koli na farko da aka shirya tun bayan da aka kara yawan mambobin kungiyar, don haka yana da ma'anar musamman. A cewar shugaban, cikin shekaru 17 bayan da aka kafa kungiyar SCO, an samu nasarori masu tarin yawa, tare da kulla abokantaka, ba domin adawa da wani bangare ba. Wannan ya taimaka wajen sabunta tsare-tsaren huldar kasa da kasa, da ba da gudunmowa ga kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin da kasashe mambobin SCO suke ciki.

A nasa bangare, Dmitrii Lukiantsev, mashawarcin jakadan kasar Rasha a kasar Sin, kuma zaunannen wakilin kasar Rasha a sakatariyar kungiyar SCO, ya bayyana ra'ayinsa dangane da maganar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi, inda ya ce, "Jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi yana da ma'ana matuka, kuma ya nuna irin managartan matakan da aka tsara. Cikin jawabinsa, ya bayyana ra'ayinsa kan yanayin da ake ciki a yankinmu da kuma duniya baki daya. Ban da haka kuma, ya yi tsokaci kan hadin gwiwar da ake yi tsakanin mambobin kungiyar SCO ta fuskokin siyasa, da tsari, da tattalin arziki, gami da ala'du. Haka zalika, ya gabatar da wasu shawarwari masu kyau. A ganina, ragowar mambobin SCO za su amince da shawarwarinsa, da kuma aiwatar da su yadda ya kamata."

Cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya ce, dalilin da ya sa kungiyar SCO ke cikin wani yanayi na yakini wajen gudanar da hadin gwiwa, shi ne domin ta aiwatar da Ruhun Shanghai, wanda ya shafi ra'ayoyin amincewa da juna, da tabbatar da moriyar juna, da daidaito, da neman daidaita sabanin ra'ayi ta hanyar tattaunawa, da mutunta dukkan al'adu, tare da niyyar ganin kowa ya samu ci gaba. Saboda haka, shugaban ya jaddada cewa, abin da za a yi a nan gaba shi ne a ci gaba da kokarin hadin gwiwa karkashin jagorancin Ruhun Shanghai, don kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. Wannan furucin da shugaba Xi ya yi, a ganin Amjad Abbas, darektan sashen nazarin harkokin siyasa na jami'ar Punjab ta kasar Pakistan, zai zama jagorar aikin gudanar da hadin gwiwa cikin kungiyar SCO, inda ya ce,

"Cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya jaddada muhimmancin samun nasara tare, da ganin sakamakon da aka cimma ya amfani kowa. Hakika ya kamata mambobin kungiyar SCO su yi watsi da sabanin ra'ayi, ta yadda kowace kasa dake yankinmu ta dandana moriyar ci gaban tattalin arziki. Ban da haka kuma, a fannin yaki da ta'addanci, babu wata kasa ita kadai da za ta iya magance matsalar. Tilas ne a karfafa hadin gwiwa, kafin a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban al'umma. Saboda haka, ina ganin cewa, tsare-tsaren da shugaba Xi Jinping ya ambata game da makomar kungiyar SCO suna da ma'ana matuka."

A nasa bangare, jakadan kasar India a Sin Gautam Bambawale, ya bayyana ra'ayinsa kan rawar da kasarsa za ta taka, inda ya ce,

"Wannan shi ne karo na farko da kasar India ta halarci taron kolin kungiyar SCO a matsayin mambar kungiyar. Hakika, a shekarar da ta gabata, kasar India ta samar da gudunmowa a fannonin tsaro, da yaki da ta'addanci, da cigaban tattalin arziki, gami da musayar al'adu, wadanda suka fi janyo hankalin al'ummomin kasashen kungiyar SCO, sa'an nan a nan gaba, kasar za ta kara taka muhimmiyar rawa a wadannan fannoni."

Sa'an nan wani shehun malami a jami'ar Delhi ta kasar India, Abhishek Singh, ya ce, hadin gwiwar da ake yi cikin kungiyar SCO za ta amfanawa kasashe mambobinta har ma da duniya baki daya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China