Bisa shirin da aka tsara, Trump da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un zai yi ganawa a otel na Capelle dake tsibirin Sentosa a ranar 12 ga wannan wata, wannan zai zama karo na farko da shugabannin Amurka da na kasar Koriya ta Arewa suka yi ganawa a tarihi.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Singapore ta bayar da sanarwa a ranar 10 ga wata cewa, firaministan kasar Lee Hsien Loong zai gana da shugaba Trump a ranar 11 ga wata. Kafin hakan, a ranar 10 ga wata a fadar shugaban kasar Singapore, Lee Hsien Loong ya gana da Kim Jong Un da ya riga ya isa kasar Singapore. (Zainab)